Manufofin Kasashen Waje

A cikin wannan shirin zamungabatar muku da manufofin kasashen waje, ma’anar sa, da kuma yanda wayannan manufofin suka shafi rayuwar mu ta yau da gobe.
Sau dayawa mutane sukan yi suka game da yawan tafiye tafiye da shugaba Buhari yake yi, duk da dai ba wai ina nufin hakan abu ne me kyau ba, amman akwai dalilai da dama da suka saka yake yin hakan. Daya daga cikin wannan dalilai shine yada manufofin kasar nan da kuma gyara abota da kasar nan take dashi da kasashe da dama.