
Ƴan bindiga sun fara karɓar haraji a gurin jama’a a jihar Sakkwato
Matsalar rashin tsaro na ci gaba da ta’azzara a wasu yankunan jihar Sakkwato, inda yanzu har ‘yan bindiga sun fara sa ma wasu daga cikin kauyukan haraji tare kuma da […]
Gaba Tsakanin Makota Bello Sani
Bello Sani November 29, 2020 10
Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Intanet a Najeriya, Isa Ali Pantami, ya ce zai isar da saƙon al’umma ga Shugaba Muhammadu Buhari game da kisan mutum 43 da ‘yan Boko Haram suka yi.
A jiya Asabar ne aka samu rahoton ‘yan bindiga sun shiga gonakin mutanen kuma suka yi musu yankan rago a yankin Koshebe na Zabarmari da ke cikin Ƙaramar Hukumar Jere a Jihar Borno.
Ministan ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter bayan wani mai amfani da shafin ya roƙe shi da ya yi hakan.
“Ya Sheikh @DrIsaPantami – muna kawo kukan mu gareka. Dan Allah dan Annabi ka samu ka yi ma shugaban qasa magana. Mutum arba’in da hudu (43) ko a movie aka kashe lokaci daya abun da ban tsoro. Dan Allah a taimaka a yi wani abun a kai abun ya fara yawa,” a cewar Boss Mustapha (@__yellows).
Shi kuma Isa Pantami ya mayar masa da martanin cewa: “Muna yin hakan kuma za mu ci gaba da yi. Zan isar masa da wannan kamar yadda na yi magana da Gwamna Zulum ɗazun nan. Allah Ya ji ƙansu kuma Ya kawo ƙarshen wannan masifa.”
Yankin arewacin Najeriya na fama da matsalolin tsaro baya ga Boko Haram da suka haɗa da ‘yan fashin daji da masu garkuwa da mutane.
Rahotanni na cewa an yi garkuwa da mutum fiye da 1,500 a yankin tare da biyan kuɗin fansa masu ɗimbin yawa.
Rikicin Boko Haram ya yi sanadiyyar rasa ran mutum fiye da 36,000 sannan an rusa gidaje fiye da kashi 30 cikin 100 na Jihar Borno baki ɗaya.
BBC Hausa
Matsalar rashin tsaro na ci gaba da ta’azzara a wasu yankunan jihar Sakkwato, inda yanzu har ‘yan bindiga sun fara sa ma wasu daga cikin kauyukan haraji tare kuma da […]
Copyright Matasa Radio - by Bello Sani
Post comments (0)