play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Kannywood
  • keyboard_arrow_right Zamu faɗaɗa aiyukan hukumar tace fina-finai har zuwa dandalin YouTube

Labarai

Zamu faɗaɗa aiyukan hukumar tace fina-finai har zuwa dandalin YouTube

Bello Sani November 13, 2020 11


Background
share close

Hukumar Tace Fina-finai ta jihar Kano ta ce za ta fantsama cikin shafukan YouTube na yanar gizo domin yin farautar masu saka fina-finai da suka karya dokar hukumar.

Shugaban Hukumar, Isma’ila Na’abba Afakallah ya bayyana cewa hukumar ta gano cewa masu shirya finafinai suna fakewa da wannan dama domin kauce wa sharuddan hukumar.

” Mun gano wasu masu shirya finafinai na kauce wa bin dokokin hukumar suna saka fim batare da an duba shi a hukumar ba. Sannan hakan ya basu daman saka duk abinda suka ga dama, har da wadanda dokar hukumar bata amince da su ba.

Isma’ila Na’abba Afakallahu ya kara da cewa daga yanzu hukumar zata dira shafukan yanar gizo, wato shafin YouTube domin farautar ire-iren wadannan fina-finan.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *