play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Siyasa
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Za a fara yiwa ƴan takarar shugabannin ƙananan hukumomi gwajin shaye-shaye a Kano

Siyasa

Za a fara yiwa ƴan takarar shugabannin ƙananan hukumomi gwajin shaye-shaye a Kano

Bello Sani November 28, 2020 11


Background
share close

Gwamna Abdullahi Ganduje ya umarci dukkan wadanda suka fito takara a zabukan kananan hukumomi da ke tafe wanda aka shirya gudanarwa a ranar 16 ga watan Janairun sabuwar shekara, da su tabbata an yi musu gwajin shaye – shayen miyagun kwayoyi.

Kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Malam Muhammad Garba ne ya bayyana hakan yayin da yake yi wa manema labarai bayani kan sakamakon taron majalisar zartarwa na jihar da aka gudanar a gidan gwamnatin Kano.

Malam Muhammad Garba, ya ce Gwamnatin jihar ta yanke shawarar yin hakan ne domin tsabtace jihar Kano daga shan miyagun kwayoyi.

Ya kuma sake jaddada aniyar gwamnatin jihar karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na magance shan miyagun kwayoyi tsakanin shugabannin siyasa a fadin jihar Kano.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *