play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Tsaro
  • keyboard_arrow_right ‘Yan ta’adda na shirin kaiwa filayen jiragen sama farmaki, FG

Labarai

‘Yan ta’adda na shirin kaiwa filayen jiragen sama farmaki, FG

Bello Sani April 12, 2021 10


Background
share close

FAAN tace ta samu labarin harin da ake shirin kaiwa tashoshin jiragen sama dake kasar nan daga ma’aikatar sufurin jiragen sama

Hukumar tashoshin jiragen saman Najeriya (FAAN) ta ce ta samu labari daga ma’aikatar sufurin jiragen sama akan yunkurin harin da ake shirin kaiwa filayen jiragen sama da suke fadin kasar nan.

FAAN ta gabatar wa da shugabannin tsaron tashoshin jiragen sama wannan sanarwar.

Kamar yadda takardar wacce TheCable ta gani ta ranar 9 ga watan Afirilun 2021, za a kai hari tashoshin jiragen sama da suke Kaduna, Maiduguri, Sokoto, Kano, Abuja da Legas.

An baiwa shugabannin tsaron tashoshin jiragen saman umarnin bayyana hanyoyi da dabarun kariya daga harin sannan an nemi su yi zaman gaggawa don samar da yadda za a bullo wa lamarin.

Karin bayani na nan tafe…kudai ko kasance da radio matasa.com domin kawo muku labarai da dumi diminsa.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *