‘Yan sanda a Jihar Ogun da ke kudancin Najeriya sun kama mutum biyu a wani gidan sayar da jarirai da wata mata ke gudanarwa bayan kotu ta bayar da belinta.
Kakakin ‘yan sandan jihar Abimbola Oyeyemi ya ce wata yarinya ce da aka yaudara zuwa gidan ta gudu sannan ta kai musu rahoto.
Dakarun rundunar sun kai samame tare da ceto yara mata 10, uku daga cikinsu na da ciki, a cewar kafar talabajin ta TVC.
Ɗaya daga cikin waɗanda aka kama har da ‘yar shugabar wurin, wadda ita ma kotu ta bayar da belinta bayan zarginta da laifin safarar mutane.
Ɗaya mutumin mai nakasa ne kuma ‘yan sanda na zargin shi ne ke yi wa ‘yan matan ciki.
BBC
Post comments (0)