An tabbatar da mutuwar mutane 10 sakamakon harin da Boko Haram ta kai Damasak
An tabbatar da rasuwar fararen hula 10 a harin da yan Boko Haram suka kai a daren ranar Talata a garin Damasak, hedkwatar karamar hukumar Mobbar na jihar Borno.
Shugaban karamar hukumar Mobbar, Mustapha Bako Kolo ne ya bayyana hakan kamar yadda Channels TV ta ruwaito.
Wasu da ke zaune a sansanin yan gudun hijira da ba a tabbatar da adadinsu ba suma sun jikkata sakamakon harin a cewar Kolo.
Duk da cewa dakarun sojojin saman Nigeria da sojojin sama sun dakile harin, wasu mutane fararen hula da dama sun jikkata.
cewar majiyoyi, yan ta’addan sun afka garin a motocci suka nufi inda sansanin sojoji ya ke a Damasak a yayin da mutane suka rika tserewa.
Harin na daren jiya a Damasak shine na biyu a cikin mako guda.
Yan ta’addan sun wallafa bidiyon harin da suka kai a karshen mako a Damasak inda suke kona gine-ginen Majalisar Dinkin Duniya da wuraren ajiye abinci.
Kawo yanzu da aka wallafa wannan rahoton, rundunar sojojin Nigeria bata yi tsokaci game da batun ba.
Alkali Hadiza Shagari ta babbar kotun tarayya dake Katsina ta yankewa gagararren mai safarar miyagun kwayoyi hukunci Babbar kotun tarayya da ta samu shugabancin Mai shari’a Hadiza Shagari a ranar […]
Post comments (0)