play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Tsaro
  • keyboard_arrow_right Yan bindigar da suka sace ɗaliban Kaduna sun nemi miliyoyin kuɗin fansa

Labarai

Yan bindigar da suka sace ɗaliban Kaduna sun nemi miliyoyin kuɗin fansa

Bello Sani March 13, 2021 41


Background
share close

Yan bindigar sun kai hari kwalejin mai suna Federal College of Forestry Mechanisation ce da ke Afaka a Ƙaramar Hukumar Igabi da misalin ƙarfe 11:00 na daren Alhamis kuma suka yi awon gaba da mutum 39, 23 mata da kuma maza 16.

‘Yan fashin sun yi amfani ne da shafukan ɗaliban wajen wallafa bidiyon a Facebook. A ɗaya daga cikin bidiyon, ana iya ganin yadda ake dukan ɗaliban mazansu da matansu da tsabga a wani wuri da ya yi kama da tsakiyar daji.

“Waɗannan mutanen sun kewaye mu kuma sun ce za su kashe mu idan wani ya yi ƙoƙarin zuwa ceton mu,” in ji ɗaya daga cikin ɗaliban wanda ya yi magana da harshen Ingilishi.

Ya ƙara da cewa: “Sun yi mana duka har sun ji mana raunuka sosai. Wasu daga cikinmu na kuka saboda raunukan da suka ji. Idan gwamnati ba ta zo ta kuɓutar da mu da wuri ba, muna cikin gagarumar matsala.”

Wata mace da ta yi magana da Hausa ta bayyana cewa “‘mutanen nan sun faɗa mana cewa idan sojoji suka yi yunƙurin cetonmu, ko ɗaya daga cikinmu ba wanda zai koma gida”.

A wani bidiyon, ana iya jin ɗalibai mata da ke zaune a bayan mazan suna cewa “ku ba su kuɗin fansar kawai. su sake mu don Allah” cikin Hausa da Ingilishi.

Wasu rahotanni na cewa ‘yan bindigar sun buƙaci naira miliyan 500 a matsayin kuɗin fansa, kamar yadda wasu iyayen ɗaliban suka shaida wa jaridar Daily Trust.

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya sha bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta taɓa yi wa ‘yan fashin dajin afuwa ba, yayin da maƙwabtan jihohinsa ke cewa sun ga amfanin sulhu da su.

Sai dai, ita ma gwamnatin tarayya ƙarƙashin Muhammadu Buhari ta tabbatar da cewa ba za ta shiga maganar sulhu da ‘yan fashin daji ba.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *