play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Tsaro
  • keyboard_arrow_right Yan bindigan da suka sace daliban Kaduna sun yanke hukuncin karshe

Labarai

Yan bindigan da suka sace daliban Kaduna sun yanke hukuncin karshe

Bello Sani April 16, 2021 61


Background
share close

Iyayen daliban kwalejin aikin noma dake Kaduna, sun ce masu garkuwa da ‘ya’yansu suna neman N500m

Iyayen daliban kwalejin horar da aikin noma da gandun dabbobi dake Afaka a jihar Kaduna, sun ce an bukaci su biya kudin fansar ‘ya’yansu har naira miliyan 500 kafin a sako su.

An bukaci da su cire rai daga tallafi ko taimakon gwamnati wurin ceto rayukan ‘ya’yansu, Vanguard ta wallafa.

Duk da 10 daga cikin daliban an sako su kuma tuni suka sadu da iyayensu, sauran suna cikin daji tun a ranar 11 ga watan Maris na 2021.

A yayin tattaunawa da manema labari a Kaduna a ranar Juma’a, mai magana da yawun iyayen daliban, Friday Sani, ya ce ‘yan bindigan sun fara kiran iyayen domin karbar kudin fansa.

Kamar yadda yace, “Halin da muke ciki a yau na tashin hankali ne kuma muna kira ga duniya da su taimaka mana. Mun yi zanga-zanga kuma gwamnatin jihar Kaduna ta kira mu. Mun yi tunanin zamu ji labari mai dadi amma sai aka sanar damu cewa za a hukunta duk wanda yayi sasanci da ‘yan bindiga.”

“Wannan ne yasa muka sake fitowa a karo na biyu domin sanar da duniya halin da muke ciki duk da an kama mana tunani tare da mallakemu ta yadda aka sace ‘ya’yanmu.

“Tuni dama gwamnati ta kama mu, wasu daga cikinmu basu iya bacci ko cin abinci yayin da wasu suka samu ciwuka, don haka babu kamen da yafi haka,” Yace.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *