Yan bindiga sun sace wani jariri ɗan shekara uku tare da mata 5 a Anguwar Epe, bayan sakandiren gwamnati (GSSS) Tungan Maje, Abuja, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Wani mazaunin yankin mai suna, Ishaku, yace lamarin ya faru da misalin ƙarfe 10:23 na ranar Talata.

Ishaku ya bayyana cewa maharan sun shiga Anguwan cikin dabaru, inda suka fara harbi a sama domin su hana maƙota da jami’an tsaro kawo ɗauki.

Yace: “Yan bindigan sun shigo Anguwan daga jikin wani babban dutse dake bayan Epe, suna zuwa suka raba kansu gida-gida, kafin daga baya wasu tawagar sun kutsa cikin wani gida inda suka yi awon gaba da jariri ɗan shekara 3 da mata 5.”

Ya ƙara da cewa kafin jami’an yan sanda su ƙariso yankin tuni yan bindigan sun gama aikin su, sun tafi da waɗanda suka yi niyyar sace wa.

Tungan-Maje dake kan hanyar zuwa Zuba-Gwagwalada na cigaba da fuskantar matsi daga yan bindiga.

Kakakin hukumar yan sandan Abuja, ASP Maryam Yusuf, ta nemi a tura mata saƙo maimakon kiran waya, amma har yanzun ba ta turo amsar saƙon da aka tura mata ba.

A wani labarin kuma Ku Gyara Halinku, Ku Tabbatar da Tsaro a Najeriya Idan Kuna Son Aikin Yi, Buhari ga Matasa

Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, ga gargaɗi matasan Najeriya da su gyara halin su idan suna son aikin yi, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Buhari ya faɗi hakane yayin wata fira da yayi da kafar watsa labarai ranar Alhamis da safe.

Leave a Comment

%d bloggers like this: