Ƴan bindiga sun sace faston cocin katolika da wasu mutane a daren ranar Litinin Kaduna
Yan bindiga sun sace, Mista Anthony Dawah, Faston Cocin Katolika, mai masa girki, da matar wani mai koyar da sabbin wadanda suka karbi addinin kirista ibada a ƙauyen Kushe Makaranta a ƙaramar hukumar Kagarko a jihar Kaduna.
Lamarin ya faru ne misalin ƙarfe 2 na daren ranar Litinin a lokacin da ƴan bindigan suka kai hari a garin, rahoton The Cable.
Lamarin na zuwa ne bayan kwanaki takwas da sace mambobin cocin RCCG takwas a ranar Juma’a a hanyar Kaduna zuwa Kachia.
Mista Joseph Hayab, shugaban Kungiyar Kiristocin Nigeria ta CAN a jihar ya tabbatar wa majiyar Legit.ng afkuwar lamarin.
“An sace Reverend Fada Dawah misalin ƙarfe 2 na daren Litinin tare da mai masa girki da matar mai koyar da sabbin wadanda suka karbi addinin kirista da wasu mutane,” in ji Hayab.
“Har yanzu yana hannun yan bindigan kuma ba su kira sun faɗa inda suke ba,” ya ƙara da cewa.
Muhammad Jalige, kakakin rundunar yan sandan jihar bai ɗaga wayansa ba a lokacin da aka kira shi.
Post comments (0)