
Gaba Tsakanin Makota Bello Sani
Bello Sani December 12, 2020 12
Rahotanni daga jihar Katsina da ke Najeriya sun ce ‘yan bindiga sun kai hari a makarantar sakandaren kimiyya da ke garin Ƙanƙara inda suka sace ɗalibai da dama.
Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar wa BBC kai harin ranar Juma’a da daddare, amma ta ce ba ta da bayanai kan sace ɗaliban.
Mai magana da yawun rundunar, DSP Gambo Isa, ya shaida mana cewa tuni aka gano ɗalibai fiye da 200 da suka tarwatse suka shiga cikin daji lokacin da ‘yan bindigar suka auka wa makarantar tasu.
Ya ƙara da cewa an yi ba-ta-kashi tsakanin ‘yan bindigar da ‘yan sanda lamarin da ya kai ga “harbin ɗan sanda ɗaya amma bai mutu ba.”
A cewarsa, an tura ƙarin ‘yan sanda domin su far wa ‘yan bindigar yana mai cewa kawo yanzu suna ci gaba da ƙirga ɗaliban da suka koma makarantar daga daji a kuma waɗanda ba su dawo ba domin sanin ainihin yawan waɗanda aka sace.
Sai dai wani ganau ya shaida wa BBC cewa an sace ɗalibai da dama a harin da ‘yan bindigar suka kai.
Mutumin, wanda ba ya so mu ambaci sunansa, ya ƙara da cewa: “A gabana ‘yan bindigar suka wuce suna harbe-harbe suka shiga makarantar kuma sun sace ɗalibai da dama. Tun da yamma muka samu labarin cewa za su kawo hari kuma mun shaida wa jami’an tsaro amma ba a ɗauki mataki ba.”
Copyright Matasa Radio - by Bello Sani
Post comments (0)