Rundunar ‘yansada Jihar Kebbi ta tabbatar da mutuwar mutum 66 a karamar hukumar Danko-Wasagu tare da cewa ana fargabar adadin zai iya wuce haka.

Kakakin rundunar ‘yansanda na Jihar DSP Nafi’u Abubakar ne ya bayyana wa BBC hakan yana cewa harin ya faru ne a ranar Alhamis da misalin karfe 3 na rana, a kauyuka takwas na karamar hukumar.

A cewar kakakin kauyukan sun hada da Kimpi da koro da Dimi da Zutu da Rafin Gora da Iguenge.

Yace harin ya fi shafar manyan maza sai kuma mata, amma har yanzu ba su kai ga tantance adadin matan da abin ya rutsa da su ba.

Ko a watan jiya sai da ‘yan bindiga suka farwa karamar hukumar suka kashe ‘yan sanda tara cikin har da DOP yankin.

Leave a Comment

%d bloggers like this: