play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Tsaro
  • keyboard_arrow_right Yan bindiga sun kashe mutum 2619, sun karbi kudin fansan kimanin N1bn: Matawalle

Labarai

Yan bindiga sun kashe mutum 2619, sun karbi kudin fansan kimanin N1bn: Matawalle

Bello Sani April 3, 2021 25


Background
share close

Gwamnan Bello Matawalle na jihar Zamfara bayyana dalilin da ya sa gwamnatinsa ta ke sulhu da yan bindiga, inda yace sulhu kadai ne mafita daga matsalar tsaron jihar.

Gwamnan ya yi bayanin cewa tsakanin 2011 da 2019, yan bindiga sun hallaka mutum 2,619, sun yi garkuwa da 1,190 kuma sun karbi akalla N970 million matsayin kudin fansa daga wajen iyalan wadanda suka sace.

 

Matawalle ya bayyana hakan ne ta bakin kwamishanan labaran, Ibrahim Dosara, a Kaduna ranar Juma’a, rahoton Punch.

A cewar Dosara, Matawalle ya zabi sulhu da tsagerun yan bindigan shine don kare rayukan al’ummarsa da dukiyoyinsu.

Yace: “Gabanin hawa mulkin Bello Mohammed Matawallen Maradun a ranar 29 ga Mayu 2019, mutan Zamfara na cikin halin ha’ula’i sakamakon hare-haren yan bindiga.”

“Kashe-kashe, sace-sace, da fyade sun zama ruwan dare.”

bayyana cewa akwai kimanin yan bindiga 30,000 a jiharsa da kuma wasu jihohin Arewacin Najeriya biyar.

A cewar gwamnan, akwai akalla sansanonin tsagerun yan bindiga 100 kuma kowace sansani na da akalla yan bindiga 300.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *