Masana harkokin fasahar zamani sun bayyana cewa akwai bukatar gwamnatin Najeriya ta mayar da hankali wurin amfani da irin wannan fasaha domin shawo kan matsalolin tsaro da suke adabar kasar musamman matsalar masu garkuwa da mutane da ta zama ruwan dare.
Wani mai bincike a kan tsaro ta intanet a jami’ar Bedfordshire da ke Ingila ya ce jami’an tsaro za su iya inganta tsaro ta hanyar amfani da fasahar zamani idan suka dauki wasu matakai.
A tattaunwarsa da BBC, mai binciken, Malam Muhammad Hamisu Sharifai, ya bayyana cewa kamar sauran kasashen da suka ci gaba, a kasashe masu tasowa ma za a iya inganta tsaron ta hanyar amfani da kimiyya da fasahar na’ura mai kwakwalwa.
Ya ce akwai bangaren da ake kira ‘cyber security’, inda ta nan za a iya inganta tsaro ta bangarori biyu – bangaren da ake kira ”intelligence” wato samun bayanai na sirri, da kuma wanda ake kira ”cyber warfare” wato aikin soja ta hanyar amfani da na’ura mai kwakwalwa.
“Wadannnan hanyoyi za su iya inganta tsaro a kasa, kuma fa’idar da za a iya samu ta hanyoyin nan ita ce idan aka yi amfani da wannan kimiyya za a iya sanin kai kawo na masu laifi, za a iya samun bayanai na sirri a kan su.
Kazalika za a iya sanin lokacin da za su tafi su aikata laifi, a daidai wurin da suke, lokacin da suka aikata laifin suka gama suka shigo gari, ko kuma idan hari za a kai musu za a san a daidai wurin da suke idan ma tahowa suke yi za sani,” in ji shi.
Malam Sharifai ya kara da cewa: “Duk da wadannan hanyoyin za ka iya samun wannan bayanai, kuma idan an samu wannan zai inganta tsaro, za ka san kai kawo din su, me suke shiryawa, duk wannan abu ne da zai taimaka wajen inganta tsaro ta hanyoyin nan da na fada.
A cewarsa, a bangaren aikin soja “cyber warfare” ko kuma aikin soja ta hanyar amfani da na’ura mai kwakwalwa zai taimaka kwarai.
“Misali, akwai jirage marasa matuka da za a iya kai hari da kuma samo bayanai na masu aikata laifi ko masu tayar da hankali, ko ‘yan ta’adda.
Akwai hukumomi na gwamnati baya ga na jami’an tsaro, kamar na fararen hula, kamar hukumar da ke sa ido kan sadarwa ta Najeriya wato NCC wacce za ta iya bayar da gudumawa matuka wajen harkar inganta tsaro a kasa, saboda mafi yawa ana amfani da wayoyin salula, na’ura mai kwakwalwa da intanet wadanda duk suna karkashin wannna hukuma ne”, in ji Malam Sharifai.
Kamar yadda mai binciken ya bayyana, akwai kimiyyar da za a yi amfani da ita muddin dai masu aikata laifi za su yi amfani da wadannan kafofi ta yadda za a iya gano su cikin sauri.
Ya kuma ce ya kamata gwamnatin Najeriyai ta mayar da hankali wajen shigo da wannan tsari na harkar tsaro, ba kawai kamar yanzu da take tara kudin haraji ana amfani da su ta wasu hanyoyin ba.
Ya kara da cewa: “Ya kamata a dawo da su su kasance wani bangare na harkar tsaro. Misali, jami’an hukumar shige da ficen kayayyaki da sukan tara kudin haraji, tana kuma bangare na tsaro duk da haka tana karkashin ma’aikatar kudi, wasu kasashen su kansu ma’aikatun sadarwa suna karkashin ma’aikatun tsaro ne,” in ji mai binciken.
Masanin ya ce: “Za a iya amfani da fasahar kimiyyar wajen yaki na zamani, kasashen duniya da dama suna da wannan bangaren a tsarinsu na soja, wanda za a iya tura jirgi ba matuki ya kai hari kan abokan gaba kana ya dawo, su kuma za a iya hana su amfani da wasu makamai ko kuma a samu bayanai na sirri a kansu”.
A cewarsa: “Amma duk irin wannan yana kasancewa ne idan aka samu musayar bayanai tsakanin jami’an tsaro, dole sai an hada kai an yi aiki tare. Su bangaren jami’an tsaro masu saka farin kaya, da bangaren ‘yan sanda, da bangaren sojoji sai an samu hadin kai.”
“Kwanan nan kasar Ingila ta gabatar da abin da ake kira “cyber force” ta kuma kaddamar da shi, shi wannan cyber force din sojoji ne, ko kuma in ce wata ma’aikata ce da aka kirkire ta da za a hada da sojoji, fararen hula, ‘yan sanda da jami’an tsaron farin kaya wadanda za su yi aiki da na’ura mai kwakwalwa domin inganta tsaro a kasarsu da kuma tsare kasarsu daga hari daga waje.
Irin wannan muke bukata a Najeriya yanzu, amma fa sai an samu wannan hadin kan saboda yana da tasisir a harkar tsaro saboda ba aiki ne na bangare daya ba; sai an hada kai an samu wadannan bayanai sannan a san yadda za a yi amfani da su tun daga kan samun bayanai na sirri ya zuwa yadda za a dakile hare-haren da za su kawo, ko kuma su masu laifi yadda za a kai musu hari,” a cewarsa
Anya kuwa Najeriya ta shirya wa wannan tsari?
Duk da cewa kasashen da suka ci gaba ne suka fi bayar da muhimmanci da kuma amfani da wannan tsari na amfani da fasahar zamani wajen inganta harkokin tsaron nasu, amma kuma Malam Muhammad Hamisu Sharifai ya bayyana cewa ko shakka babu Najeriya ma za ta iya bin wannnan tsari wajen magance matsalolin tsaro a kasar.
”Kusan ma abin da ya kamata a ce tun tuni an yi kenan saboda yanzu ba wai karfi ne kawai na soja yake cin yaki ba, ko ake iya dakile matsalar tsaro da ita ba, ana amfani da hikima, tunani da ilmi na zamani ne yanzu.
Misali, idan masu aikata laifi ko ta’addanci sun dauki bindiga, ‘yans anda ko sojoji sun dauki bindiga, irin wannan sai a dade ba a magance matsalolin da suka kamata ba, don kowa abu daya yake yi, amma idan ya zamanto an sa ilmi da fasaha da kimaiyya na zamani, za a iya samun bayanan sirri na abubuwa, wanda masu aikata laifi ba za su iya samun wannan damar ba tun da akwai wasu ma’aikatu da ke lura da wadannan abubuwa da wani bai isa ya kirkiro nashi na kan sa ba,” in ji shi.
Matsalolin rashin tsaro na ci gaba da addabar Najeriya musamman arewacin kasar inda ‘yan bindiga da mayakan Boko Haram da masu garkuwa da mutane suka kashe dubban mutane sanna suka raba miliyoyi da gidajensu.
BBC
Post comments (0)