play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Tsaro
  • keyboard_arrow_right Cin Zarafi
  • keyboard_arrow_right Yadda sojojin ƙasar Kamaru suka yi wa mata 20 fyaɗe a wani harin ramuwar gayya

Tsaro

Yadda sojojin ƙasar Kamaru suka yi wa mata 20 fyaɗe a wani harin ramuwar gayya

Bello Sani February 27, 2021 33


Background
share close

Kungiyar Kare Hakkin Bil’adama ta Human Rights Watch ta ce ta tattara shaidu na harin daukar fansa da aka kai kusan shekara daya baya, da sojojin Kamaru suka kai a wani kauye inda suka yi wa mata akalla 20 fyade.

Sumamen da aka kai Ebam a yankin da ‘yan aware ke fafutukar kafa kasar Ambazonia mai cin gashin kanta, na daya daga cikin munanan ayyukan da sojojin Kamaru suka aikata a shekarun baya, in ji kungiyar.

Ba a bayar da rahoto sosai ba saboda kyama da tsoron daukar fansa wanda ke hana wadanda suka tsira daga cin zarafin yin magana.”Shekara daya da faruwar wannan lamari, wadanda suka tsira daga harin na Ebam suna matukar bukatar adalci da biyan diyya, kuma suna rayuwa cikin kunci duba da cewa wadanda suka ci zarafinsu suna yawo a garikuma ba su fuskanci wani sakamako ba,” in ji Ida Sawy’er na kungiyar.

Binciken na HRW ya hada da tattaunawa tsakanin watan Agusta da Janairu tare da shaidu, wadanda suka tsira daga fyade da kuma wani likita da ya kula da su.

Shaidu sun ce sama da sojoji 50 sun shiga Ebam da kafa da misalin karfe 03:00 na ranar 1 ga Maris 2020, inda suka kutsa kai kusan dukkanin gidaje 75 na kauyen.Wasu sojoji sun tara maza, yayin da wasu suka yiwa mata fyade, ciki har da nakasassu hudu, in ji HRW.

An tsare mutane da yawa kuma an yi musu mummunan duka kuma sojoji sun kashe wani mutum mai shekaru 34 a cikin wani daji a ƙauyen, inji kungiyar.

“Wasu sojoji biyar da suka rufe fuskokinsu sun shiga gidana,” a cewar wata mace mai shekaru 40 da ta bada shaida.

“Dare ya yi a lokacin, ni kadai ce a gida, .amma suka bincike gida, suka sace wayata da kuɗi. Daya daga cikinsu ya zage ni. Ya ce: ‘Idan ba ku yi lalata da ni ba, zan kashe ku!’

“Na ji tsoron fada ko aikata wani abu. Bayan fyaden, na gudu zuwa cikin daji inda na yi watanni biyu. Har yanzu ina cikin bacin rai da damuwa. “Shaidu sun ce aikin na sojan ramuwar gayya ne don hukunta fararen hular da ake zargi da hada kai da mayakan ‘yan aware.Kakakin rundunar ya yi watsi da rahoton.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *