
Ranar komawa makaranta na wasu jami’ar Bayero
Wasu jami’o’in gwamnati a Najeriya sun fara shirye-shiryen koma wa makaranta daga ranar 18 ga watan Janairun 2021. Hakan na zuwa ne bayan janye yajin aikin da aka shafe dogon […]
Gaba Tsakanin Makota Bello Sani
Ana ci gaba da tafka muhawara a jihar Kano da ke arewacin Najeriya game da zargin da ake yi wa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na cefanar da wasu daga cikin ƙadarorin gwamnatin jihar.
Ya zuwa yanzu ana cewa an sayar da yawa daga cikin ƙadarorin jihar baki ɗaya, wasu kuma an sayar da wani sashe nasu, yayin da ake tattauna yadda za a cefanar da wasu a nan gaba.
Sai dai Gwamna Ganduje da Kwamishinansa na yaɗa labarai Muhammad Garba na fitowa akai-akai suna cewa ba sayar da wuraren ake yi ba, ana ba da su ne ga masu bunƙasa birane zuwa wasu ‘yan shekaru kafin daga bisani su koma ƙarƙashin ikon gwamnatin jihar ta Kano.
Amma da yawa daga cikin masu yaƙi da wannan manufa kamar su dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a 2019 Injiniya Abba Yusuf, da ya shigar da gwamnatin Kano ƙara a baya, kan zargin cefanar da ƙadarorin, suna cewa ana yin abubuwa ne a ƙudundune ba a bari mutane su san halin da ake ciki.
Kungiyoyi da ɗaiɗaikun mutane na sukar wannan mataki tare da yunƙurin lalubo hanyoyin da za a dakatar da wannan mataki na Gwamna Abdullahi Ganduje.
Kamfanin gidan jarida na Triumph: Wannan kamfanin shi ke buga jaridar Triumph da kuma Alfijir da ake bugawa da Ajami, yana daga cikin wuraren da ake zargin an sayar da su baki daya.
Ana ruwaito cewa gwamnati ta ce ba a amfani da ginin kamfanin yadda ya kamata, shi yasa ta yanke shawarar bai wa ‘yan kasuwar musayar kudi ta Wapa su ci gaba da amfani da shi.
Filin fakin na Shahuci: Wannan filin an gina shi da jimawa kuma irin ginin zamani da za a rika ajiye motoci da sauran ababen hawa na masu sana’a a kewayen wajen, domin samun kudaden shiga ga gwamnatin jihar.
Amma maganar da ake yi a yanzu an rushe ginin wajen baki daya, kuma hakan ya dugunzuma ran al’ummar jihar ganin cewa an yi almubazzaranci da kuɗaɗe.
Otel ɗin Daula: Dadadden otel ne mallakar jihar Kano da ake saukar bakin jihar ko kuma ake bayar da shi cikin sauki ga masu son amfani da shi, domin samun kudaden shiga.
Makarantun Sakandire: Mafi yawan jikin katangar makarantun sakandiren da ke jihar Kano ana zargin an sayar da su domin kuwa zaka ga shaguna a jikinsu ta ko ina an fitar, ‘yan kasuwa duk sun kama suna ci gaba da harkokinsu.
Kukan da masu suka ke yi shi ne, lokacin da yara ke cikin aji suna karatu su kuma ‘yan kasuwa sun tayar da injinansu na wuta ko kuma suna harkokin kasuwancinsu, wanda hakan zai iya cutar da yaran da kuma yanayin karatunsu.
Filin wasa na Sabon Gari: Filin wasan kwallon kafa da kungiyar Kano Pillars ke buga wasanninta ciki shima an sayar da mafi yawan katangar da ta kewaye shi ga ‘yan kasuwa.
Masallacin Idi na Kofar Mata: Filin cikin masallacin da kuma kewayensa ya zama cikakkiyar kasuwa wani bangaren kasuwar sai da kayansawa ta kwari, wani bangaren kuma kasuwa Kofar Wambai.
A ganin gwamnatin jihar bai kamata a bar wuri mai girma kamar na masallacin ba zaune haka, lokacin da take ta fafutukar samun kudaden shiga domin bunkasa rayuwar mutanen jiharta.
Masallacin Juma’a na Waje (Fagge): Shi na an sayar da wani sashe nasa, baya ga zabtarar wani sashe da aka yi, domin fadada gadar saman da ta tashi daga wapa zuwa titin maganda.
Gidan Ajiyar Namun Daji (Zoo): Labarin za a sayar da wannan gida ya janyo cece-kucen da duk na baya ba su janyo ba, domin kuwa kungiyoyin kare hakkin dan adam da na masu rajin kare muhalli da tsirrai duk sun tofa albarkacin bakinsu kan wannan batu.
Wasu na ganin a cikin kwaryar birnin Kano babu wani waje da ke da dausayi sama da wannan gida, idan kuma aka sare su zai zama cutarwa ga muhalli.
Sai dai gwamnatin jihar ta ce so take ta sauyawa dabbobin wuri domin tausayawa halin da suke ciki, ganin mutane sun cimmusu, ba kuma sa samun irin iskar da ya kamata su samu.
Gidan Zakka: Wannan ne wuri na baya bayan nan da ake zargin gwamnatin da bayyana aniyarta ta sayar da shi, ko da yake gwamnatin ta ce wani ɓangare ne na jikin ginin za ta yi amfani da shi amma ba ainihin ginin gidan ba.
Masu lura da gidan sun yi alƙawarin ba za su ƙyale wannan lamari ba, suna cewa za su shigar da ƙara gaban kotu domin hana wannan mataki.
Wasu jami’o’in gwamnati a Najeriya sun fara shirye-shiryen koma wa makaranta daga ranar 18 ga watan Janairun 2021. Hakan na zuwa ne bayan janye yajin aikin da aka shafe dogon […]
Copyright Matasa Radio - by Bello Sani
Post comments (0)