play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Kiwon Lafiya
  • keyboard_arrow_right WHO ta gargaɗi Musulmin Duniya kan ƙaratowar Watan Azumin Ramadhan

Labarai

WHO ta gargaɗi Musulmin Duniya kan ƙaratowar Watan Azumin Ramadhan

Bello Sani April 4, 2021 11


Background
share close

Kwanaki kaɗan kafin zuwan watan Ramadan da kuma na ista, ƙungiyar lafiya ta duniya (WHO) ta gargaɗi musulman duniya kan dokokin kare yaɗuwar korona.

WHO ta ce ya kamata ƙasashen da suke fuskantar ƙaruwar masu kamuwa da cutar su ɗage waɗannan bukukuwan ko kuma su rage yawan jama’an da zasu haƙarci wurin.

Ƙungiyar ta ce duk wani taron addini da za’ai a fili wanda zai tara jama’a, kamata ya yi a ƙayyade jama’an da zasu harci wurin.

wajen to ya kiyaye ka’idojin kare yaɗuwar cutar COVID19, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

Ƙungiyar ta shawarci al’umma da cewa, zai fi ma jama’a kyau su yi bikinsu a cikin gida tare da waɗanda suke rayuwa tare. Su guje ma haɗuwa da sabbin mutane musamman waɗanda basu da lafiya.

Duk wani taro da zai haɗa mutane kala daban-daban to yanada hatsari,” cewar WHO.

Masana na tsoron mutane za su iya aje ƙa’idojin kariya daga kamuwa da cutar COVID19 a ya yin da suke gudanar bikin addinin su.

A kwanaki kaɗan masu zuwa kiristoci zasu gudanar da bikin ista, haka kuma ana sa ran musulmi za su fara ibadar azumin ramadan a ran 13 ga watan Afrilu.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *