play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Soyayyar Zamani
  • keyboard_arrow_right Uwargida Ta Kona Mijinta Da Amaryarsa

Labarai

Uwargida Ta Kona Mijinta Da Amaryarsa

Bello Sani February 17, 2021 7


Background
share close

Wata matar aure ta shiga hannu bisa zargin ta da kona kishiyarta da mijinta ta hanyar cinna musu wuta a dakin da suke kwance.

Ita dai amaryar wadda jikinta ya sale baki daya a sanadiyar wutar, kwana 9 ke nan da daura masu aure da mijin nata wanda shi ma gefen jikinsa ya sale, a wannan wutar da aka cinna musu.

Wannan abu ya faru ne a kauyen Sheni da ke Karamar Hukumar Lere a Jihar Kaduna.

Wasu mutanen da suke zaune a gidan da wannan al’amari ya faru ne sun zargi uwargidar da yin wannan aika-aika bisa kalaman da ta rika yi, kafin faruwar wannan al’amari kamar yadda suka bayyana.

Da yake bayyana wa Aminiya yadda al’amari ya faru a kan gadon da yake kwance a asibiti, mijin matar ya ce an cinna wutar ce ta kofar dakinsu da misalin karfe 12 na daren ranar Lahadin makon jiya.

Ya ce suna zaune a bakin gado sai ya ga wuta a kofar dakinsu.

Nan take ya tashi zai bude kofar dakin, sai ya ya gagara, sakamakon haka ne ya kone a gefan hannunsa.

Ya ce ya sake komawa zai bude dakin amma ya sake gagara.

“Sai matar tawa ta bude tagar dakin, sai na ce bari na fara tura ki ki fita, sai ta ce a’a kai ka fara fita.

“Na yi kokarin in fara tura ta, sai ta ce a’a, ni ne zan fara fita, sai na cusa kaina tana turo ni, wani kanina yana ja na daga waje.

“Bayan da na fita aka yi kokarin a fito da ita, abu ya gagara, sai da wutar ta gama ci sannan aka fito da ita.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *