play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Tsaro
  • keyboard_arrow_right Tashin hankali a Kaduna yayin da wasu ‘yan fashi suka sace mambobin RCCG 8

Labarai

Tashin hankali a Kaduna yayin da wasu ‘yan fashi suka sace mambobin RCCG 8

Bello Sani March 27, 2021 8


Background
share close

Akalla mambobin Cocin Redeemed Christian Church of God takwas yan bindiga suka sace a Kaduna, a ranar Juma’a, 26 ga watan Maris.

Jaridar The Punch ta rahoto cewa wadanda lamarin ya rutsa da su suna cikin motar cocin ne suna tafiya domin halartan wani taro lokacin da aka kai musu harin.

Legit.ng ta tattaro cewa wani mai amfani da Facebook, Eje Kenny Faraday, ya sanar da labarin a shafinsa tare da hoton farar motar a yammacin ranar Juma’a, 26 ga Maris.

Ya rubuta cewa:

“Dukkan fasinjojin da ke cikin wannan motar an yi garkuwa da su ne a kan titin Kachia, kilomita 63 daga Kaduna.”

Jaridar ta kuma lura da cewa wata majiya ingantacciya da kuma wani jami’in cocin, wanda suka yi magana bisa sharadi sakaya sunansu, sun tabbatar da rahoton.

An ruwaito majiyar ta ce: “Su takwas ne a cikin bas din. Za su je Kachia a shirye-shiryen cocin na bikin Ista. ‘Yan bindigar sun fitar da su daga motar bas din sannan suka sanya su a cikin motarsu na aiki. Har yanzu ba su tuntubi cocin ba. ”

A cewar rahoton, jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan jihar, Mohammed Jalige, ya ce yana ci gaba da bincike kan lamarin.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *