play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Tsaro
  • keyboard_arrow_right Suna hanamu Sallah, kullum sai sun buge mu: Cewar Daliban da suka samu kubuta a Kaduna

Labarai

Suna hanamu Sallah, kullum sai sun buge mu: Cewar Daliban da suka samu kubuta a Kaduna

Bello Sani April 10, 2021 22


Background
share close

Daya daga cikin dalibai kashi na biyu da yan bindiga suka saki bayan sacesu da aka a makarantar ta FCFM dake Afaka, Kaduna, AbdulGaniyu Aminu, ya ce yan bindigan na hanasu Sallah kuma kullum suna bugunsu.

Bayani kan abubuwan da suka fuskanta cikin makonni uku da sukayi a daji, AbdulGaniyu ya ce bai taba shan wuya irin wannan a rayuwarsa ba.

Yayi wannan bayani ne jim kadan bayan gwamnatin jihar ta mikasu ga shugabannin makarantar.

“Cikin makonni uku da na yi a daji ban yi wani baccin kwarai ba. Ta yaya ma zakayi bacci saboda suna hanamu Sallah kuma suna zanemu tare da buga mana gindin bindiga,” yace.

A cewar Daily Trust, sunayen dalibai biyar kashi na biyu da aka sako sune Suzan Jatau, Ishaya Jafaru, Abdulganiyu Aminu, Haruna Aminu da Adamu Amin.

A jawabin kwamishana tsaro da harkokin cikin gidan jihar, Samuel Aruwan, ya yi kira ga daliban kada su yadda wannan ya karya musu gwiwa su ce zasu daina karatu.

Jiya kun ji cewa an sake sakin wasu dalibai biyar cikin 39 da aka sace a makarantar FCFM Afaka, jihar Kaduna.

Wannan ya biyo bayan mutum biyar da aka saki ranar Litinin.

Adadin daliban Afaka da aka saki yanzu ya zama 10, har yanzu akwai sauran 29 hannun yan bindiga.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *