play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Tsaro
  • keyboard_arrow_right Sojoji sun yi artabu da ‘yan ta’addan Boko-Haram/ ISWAP da ke kwasar ganima a Damasak a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Labarai

Sojoji sun yi artabu da ‘yan ta’addan Boko-Haram/ ISWAP da ke kwasar ganima a Damasak a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Bello Sani April 12, 2021


Background
share close

Sojojin kasa tare da taimakon jiragen sama na rundunar sojin sama sun yi bata kashi da ‘yan ta’addan Boko Haram a Damasak, hedkwatar karamar hukumar Mobbar na jihar Borno.

Kafar watsa labarai ta PRNigeria ta tattaro cewa ana zargin wasu daga cikin yan ta’addan suna kan kwasar ganima yayin da suka afka wa rumbunan ajiyar kungiyoyin agaji na kasa da kasa a cikin motocinsu.

Wani jami’in leken asiri ya ce ‘yan ta’adda sun zo a cikin manyan motocinsu suna kai hari kan rumbunan ajiyar kafin isowar jirgin sojan.

“Labari mai dadi shine cewa jirgin rundunar sojin sama ya kai mu su hari ta sama yayin da aka jibge sojojin kasa a wasu wurare masu muhimmanci suna musayar wuta”, in ji majiya

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *