play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Siyasa
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Shugaba Buhari ya ba mutane 5 mukamai kafin ya bar Najeriya, ya tafi ganin Likita a Ingila

Siyasa

Shugaba Buhari ya ba mutane 5 mukamai kafin ya bar Najeriya, ya tafi ganin Likita a Ingila

Bello Sani March 31, 2021 10


Background
share close

Shugaba Muhammadu Buhari ya nada sababbin shugabanni a hukumar NASENI mai kula da kirkiren kimiyya da fasaha a Najeriya.

Shugaban kasar ya yi wannan sauya-sauye ne a yunkurin gwamnatin tarayya na ganin an gyara wannan ma’aikata domin ta yi aiki da kyau.

Nadin da shugaba Muhammadu Buhari ya yi, ya fito ne ta ofishin babban ma’aikacin fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim A. Gambari.

Jaridar ta ce fadar shugaban kasa ta sanar da shugaban ma’aikatar NASENI game da wannan nadin mukamai da mai girma shugaban kasa ya yi.

Kamar yadda ma’aikatar ta NASENI ta bayyana a wani jawabi da ta fitar a ranar Litinin, wasikar shugaban kasar ta samu shigo wa hannunta.

Mai magana da yawun bakin NASENI, Olusegun Ayeoyenikan ya bayyana haka a wata sanarwa.

Adunni Komolafe, sakatafiyar ma’aikatar, sai Injiniya Farfesa Danshehu Bagudu Gwandangaji.

Sai kuma Farfesa Umar Ibrahim Gaya, Misis Nonyem Onyechi, da Mista Ibrahim Baba Dauda.

Darektcoin za su kula da harkar fasahan, gudanar wa, tsare-tsare, cigaban kasuwanci, da harkar kudi. Za su yi shekara biyar a wannan kujeru.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *