play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Siyasa
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Rabi’u Kwankwaso: Tsohon gwamna ya ce jama’ar Kano sun fi bukatar ilimi ba gada ba

Siyasa

Rabi’u Kwankwaso: Tsohon gwamna ya ce jama’ar Kano sun fi bukatar ilimi ba gada ba

Bello Sani March 26, 2021 19


Background
share close

Tsohon Gwamnan jihar Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya, Senata Rabiu Musa Kwankwaso ya soki lamirin gwamna mai ci, Abdullahi Ganduje game da shirin gwamnatinsa na karbar rancen naira biliyan ashirin don aiwatar da aikin gina gada a birnin Kano.

Senata Kwankwaso ya ce ba dai-dai ba ne gwamnati ta ci bashin da zai bar al`ummar da za a haifa nan gaba da dawainiyar biya.

A tattaunawarsa da BBC, tsohon gwamnan Kanon ya ce hakkin gwamnatin tarayya ne ta gina gadar, wadda ta hada birnin Kano da hanyar zuwa Wudil.

A cewarsa, “maimakon gwamna ya je ya ga Buhari ya ce da shi ka zo ka yi mana gada, bai yi ba, gadojin da muka yi a Kano gaba dayansu da kudin gwamnatin wannan lokaci muka yi”.

Kwankwaso ya kara da cewa duk da ana bukatar gada a Kano, amma abin da mutanen jihar suka fi bukata shi ne ilimi – “a koya wa yayan talakawa aikin sana’oi na hannu wanda yara za su iya rike kansu”. in ji sa.

Ya kuma soki yadda gwamna Ganduje yake sayar da filaye lamarin da a baya-bayan nan ya janyo ce-ce-ku-ce.

Da yake magana kan makomar filayen da gwamnatin Kano ke sayarwa kuwa, tsohon gwamnan jihar Kanon ya bayyana cewa matukar mulki ya koma hannunsu, toh ba makawa sai an rushe gine-ginen da aka aza kan filayen.

“Duk wani gurin hukuma, mutum ko ya yi bene hawa dubu a ruguzo shi, a share gurin a mayar da shi yadda yake da”, a cewar Kwankwaso.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *