play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Siyasa
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo ya ci gyaran matakin da Buhari, CBN, su ka dauka

Siyasa

Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo ya ci gyaran matakin da Buhari, CBN, su ka dauka

Bello Sani February 26, 2021 21


Background
share close

A yau Juma’a ne mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya yi kira a sa ido a yadda ake amfani da kudin ‘cryptocurrency’ a Najeriya.

Jaridar Vanguard ta rahoto Yemi Osinbajo ya na cewa abin da ya dace ayi shi ne a gyara harkar kudin yanar gizon, a maimakon a hana aiki da shi.

Farfesa Osinbajo ya bayyana haka ne a lokacin da ya tattauna a kan abubuwa da-dama, daga ciki har da sha’anin kimiyya da fasahar kudin yanar gizo.

“Game da fasahar kudin yanar gizo da dukiyar cryptocurrencies, bari in fadi abubuwa biyu: na farko babu tantama cewa a nan da wasu ‘yan shekaru, fasahar blockchain za ta zama kalubale ga yadda aka saba aikin banki har da adanan kudi ta yadda ba a tunani.”

“Game da fasahar kudin yanar gizo da dukiyar cryptocurrencies, bari in fadi abubuwa biyu: na farko babu tantama cewa a nan da wasu ‘yan shekaru, fasahar blockchain za ta zama kalubale ga yadda aka saba aikin banki har da adanan kudi ta yadda ba a tunani.”

“Saboda haka dole mu shirya wa wannan sauyi da za a samu, kuma ya na nan zuwa ba da dade wa ba.”

“Yanzu haka ana yi wa kafofin cire kudi barazana, fasahar blockchain ya kawo damar da ta fi araha wajen aika kudi daga kasa zuwa kasa.” Inji Osinbajo.

Osinbajo yake cewa irinsu tsarin Ripple, sun zo wa bankunan da aka saba aiki da su da matsaloli.
“Na yaba da mataki mai tsauri da CBN, SEC da wasu hukumomi suka dauka domin hana yin ta’adi da cryptocurrencies, amma ya kamata su sake tunani.”

“Akwai bukatar a sa ido ne a nan.” Osinbajo ya yi kira a sa-ido a madadin a kawo dokar haramci. Ya ce: “Mu yi kaffa-kaffa wajen rungumar wannan fasaha.”

Kwanaki daya daga cikin ‘ya ‘yan mataimakin shugaban Najeriya, Yemi Osinbajo mai suna Fiyin Osinbajo, ya yi dogon rubutu a game da tsarin Cryptocurrencies.

A rubutunsa, Fiyin Osinbajo ya bayyana irin moriyar da ake ciki da tsarin Cryptocurrencies, ya ce bai kamata CBN ya hana mu’amala da wannan kudi a Najeriya ba.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *