play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Siyasa
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Kaiwa Gwamna Ortom hari: Rundunar Kyari ta dira jihar Binuwai

Siyasa

Kaiwa Gwamna Ortom hari: Rundunar Kyari ta dira jihar Binuwai

Bello Sani March 29, 2021 19


Background
share close

Tawagar DCP Abba Kyari ta dira jihar Binuwai domin tsamo wadanda suka kaiwa Gwamna Ortom hari

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tabbatar da isar tawagar garin Makurdi dake jihar Binuwai domin cigaba da bincike. Kamar yadda Frank Mba, kakakin rundunar ya sanar, IGP ya bukaci tawagar ta hada kai da ‘yan sandan jihar domin bincike

A kokarin tabbatar da binciken da ya dace tare da damke masu hannu a harin da aka kaiwa gwamman jihar Binuwai, Samuel Ortom, sifeta janar na ‘yan sandan Najeriya, IGP Mohammed Adamu ya tura gagarumar rundunarsa daga Abuja zuwa Binuwai karkashin shugabancin DCP Abba Kyari.

IGP Adamu ya bukaci rundunar da su nuna kwarewarsu da hazakarsu yayin bincike, jaridar Leadership ta bayyana.

A yayin tabbatar da sahihancin labarin, kakakin rundunar ‘yan sandan, Frank Mba yace, “Sifeta janar na ‘yan sandan Najeriya ya kafa gagarumar rundunar bincike domin cigaba da aiki kan rahoton hari da yunkurin kashe Gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom. Rundunar ta isa garin Makurdi.

Tawagar da ta samu jagorancin DCP Abba Kyari, ta hada da jami’an FIB da sauran kwararru da suka kasance zakaru wurin binciken masu laifi.

“Ana tsammanin tawagar za ta dasa daga kan bincike da aka fara kan lamarin.”

Tawagar za ta binciki duk wani lungu da sako na harin tare da tabbatar da ta bankado duk wasu masu alaka da lamarin.

“Ana tsammanin za su yi aiki tare da rundunar ‘yan sandan jihar Binuwai da sauran jami’an tsaro wurin tabbatar da sun yi aiki mai kyau.”

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *