play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Kiwon Lafiya
  • keyboard_arrow_right Chris Ngige ya sanar da matakin da FG za ta dauka kan likitoci masu yajin aiki

Labarai

Chris Ngige ya sanar da matakin da FG za ta dauka kan likitoci masu yajin aiki

Bello Sani April 3, 2021 5


Background
share close

Gwamnatin tarayya zata tilasta dokar dakatar da albashi matsawar ma’aikaci bai yi aikinsa ba ga kungiyar likitoci masu neman kwarewa na Najeriya basu koma kan ayyukansu ba.

Ministan ayyuka da kwadago, Chris Ngige ne ya sanar da wannan jan kunnen a ranar Juma’a a wata tattaunawa da gidan talabijin din Channels.

“A ranar Talata, zan gayyacesu don su koma kan ayyukansu. Zan sanar dasu cewa matsawar ba su yi aiki ba gwamnati ba za ta biyasu ba,” cewar Ngige.

Wadanda aka dauka aiki ya kamata su dage wurin kulawa da lafiyar marasa lafiya. Za mu iya neman likitocin gargajiya, bana fatan mu kai nan wurin amma in dai aka kai toh za mu yi amfani da tsumagiyarmu.”

 

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *