play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Siyasa
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Boko Haram da ‘yan bindiga: Ministan Buhari yace an samu zaman lafiya a Najeriya

Siyasa

Boko Haram da ‘yan bindiga: Ministan Buhari yace an samu zaman lafiya a Najeriya

Bello Sani March 31, 2021 8


Background
share close

Ministan ya sanar da hakan ne yayin ziyarar da kwamitin tsaro na majalisar tarayya ya kai masa

Magashi yace da tallafin majalisar dattawa tare da na ma’aikatarsa, kalubalen tsaron kasar nan zai zama tarihi

Bashir Magashi, ministan tsaro, ya ce kasar nan na fuskantar zaman lafiya duk da irin kalubelen tsaro da take ciki.

Rundunar sojin kasar nan sun kasance suna yaki da Boko Haram a yankin arewa maso gabas sama da shekaru 10.

The Cable ta ruwaito cewa, dakarun suna cigaba da gwagwarmaya da ‘yan bindigan da suka addabi yankin arewa maso yamma da sauran sassan kasar nan.

A yayin karbar kwamitin majalisar dattawa a kan lamarin tsaro a ranar Talata, ya ce an kashe jami’an tsaro a wasu wurare amma duk da haka rundunar sojin kasar nan ta samu nasara.

“Najeriya tana fama da matsalar tsaron cikin gida sakamakon addabar da mayakan Boko Haram suka yi a arewa maso gabas da kuma ‘yan bindiga a jihohin Niger, Katsina, Kaduna, Sokoto da Zamfara,” yace.

“Wadannan kalubalen sun matuukar zama dalilan da suka sa muke rasa zakakuran dakarunmu dake kan aiki.”

Magashi yace da taimakon majalisar dattawa, ma’aikatarsa za ta cigaba da aikin da ya dace tare da samun zaman lafiyan da Najeriya ke bukata.

A bangarensa, Aliyu Wamakko, wanda ya jagoranci kwamitin majalisar, ya ce yana da tabbacin Najeriya za ta shawo kan matsalolin tsaro da suke ci mata tuwo a kwarya.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *