play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Siyasa
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right An Sa Gasar Kwaikwayon Daurin Dankwalin Ngozi Okonja-Iweala A Twitter

Siyasa

An Sa Gasar Kwaikwayon Daurin Dankwalin Ngozi Okonja-Iweala A Twitter

Bello Sani February 16, 2021 25


Background
share close

Wata ’yar kasuwa mai amfani da dandalin sada zumunta na Twitter mai suna Temi Giwa-Tubosin, ta sanya gasar kwaikwayon daurin dankwalin tsohuwar ministar kudin Najeriya, Ngozi Okonja-Iweala.

Ms Giwa-Tubson ta wallafa sakon sanya gasar ne a shafinta na Twitter, inda ta daurin kallabi irin na tsohuwar minister sannan kuma tana jawabi a kan tattalin arziki kamar yadda aka san Ngozi da yi.

Temi ta yi alkawari bayar da kyautar naira dubu dari ga duk wanda ya fi dacewa da kwaikwayon daurin dankwalin tsohuwar minister.

Da dama daga cikin mabiya shafin na Twitter, suna ci gaba da aika hotunansu da daurin kallabi a kokarinsu na kwaikwayon tsohuwar minister kudi da ta yi zamani a gwamnatin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.

Al’ummar Najeriya da dama da kuma na kasashin Afrika har ma da na ketare, na ci gaba da bayyana alfaharinsu da nuna goyon bayan a kan Ms Ngozi, mace ta farko da ake sa ran za ta zama Shugabar Kungiyar Cinikayya ta Duniya.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *