Shugaban kasar Japan ya nada ministan kadaici a kokarinsa na rage kadaici da hana kebance kai a tsakanin mazauna kasar domin rage yawan masu kashe kansu.
Kamar yadda The Japan Times ta ruwaito, Firayim minista Yoshihide Suga ya kirkiro kujerar a watan Fabrairu bayan Ingila ta kirkiro mukamin a shekarar 2018.
Kiyasi daga rundunar ‘yan sandan kasar ya nuna cewa mutum 20,919 ne suka kashe kansu a 2020, karin mutum 750 da aka samu a shekarar da ta gabata. Kamar yadda aka gano, yawan wadanda ke kashe kansu sun fi a mata da matasa.
The Times ta ce Japan ta san da kadaicin da ake kira da kodukushi ko kuma ‘mutuwar kadaici’ an saba ganinsu a Japan. Jama’a na mutuwa a gidajensu kuma ba a sanin sun mutu sai bayan wani lokaci.
An gano cewa Japan ce kasar da take da mutane masu shekaru 60 zuwa sama da suke jin basu da wanda za su komawa a lokutan bukata.
A watan Oktoba, Japan ta fuskanci mutuwar jama’a wadanda suka kashe kansu fiye da yawan wadanda cutar korona ta kashe a 2020.
A watan Oktoban 2020 kadai, an samu mutum 2,153 da suka kashe kansu a Japan yayin da cutar korona ta kashe mutum 1,765 a dukkan shekarar.
Post comments (0)