
Gaba Tsakanin Makota Bello Sani
Shugaban kasa kasar Najeriya Muhammadu Buhari zai hallara gaban zaman majalisun dokokin tarayyar kasar a jibi Alhamis domin yin jawabi kan batun harkokin tsaro.
Hakan na cikin wani jawabi da mai taimaka wa shugaban kasa Muhammdu Buhari kan kafofin sada zumunta, Lauretta Onochie ta wallafa a shafinta na Twitter.
Ana tunanin jabawabin shugaban zai mayar da hankali kan matsalar tsaro da ke damun arewacin kasar.
A makon da ya gabata mayakan Boko Haram suka kashe Manoma arba’in da uku a Zabarmari jihar Borno tare da yanka wasu bakwai a jihar Katsina da tafiya sama da talatin, wanda haka ya sanya majalisar wakilai ta gayyaci shugaban don ya hallara a gabanta wanda kuma ya amsa goron gayyatar.
Copyright Matasa Radio - by Bello Sani
Post comments (0)