play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Satar Doya Ta Jawo Masa Hukuncin Bulala 12 A Kotu

Labarai

Satar Doya Ta Jawo Masa Hukuncin Bulala 12 A Kotu

Bello Sani February 12, 2021 11


Background
share close

Wata Babbar Kotun Lardi dake zamanta a yankin Zuba na Babban Birnin Tarayya Abuja ta yanke wa wani matashi hukuncin bulala 12 saboda satar doya.Wata Babbar Kotun Lardi dake zamanta a yankin Zuba na Babban Birnin Tarayya Abuja ta yanke wa wani matashi hukuncin bulala 12 saboda satar doya.

Tun da farko dai ’yan sanda sun zargi matashin wanda mazaunin Garejin Dankogi ne da laifin sata.
Da yake yanke hukunci, alkalin kotun, Mai Shari’a Gambo Garba ya shawarci matashin da ya canza halinsa.

Dan sanda mai shigar da kara, Chinedu Ogada ya shaidawa kotun cewa Hashimu ya aikata laifin da ake zarginsa ne ranar 26 ga watan Disambar 2020, bayan wanda aka yi wa satar, Tanko John ya kai kara ga ofishin ’yan sanda na Zuba

Chinedu ya shaidawa kotun cewa Hashimu ya tsallaka gonar Tanko ne dake Zuba ya kuma sace doya ta kusan wannan adadin.

Ya ce binciken yayin binciken ’yan sanda na farko-farko, Hashimu ya amsa laifin da ake zarginsa da aikatawa kuma tuni aka karbe kayan satar daga hannunsa.

Laifin, a cewar dan sandan ya saba da tanade-tanaden sashe na 287 na kundin Penal Code.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *