Masarautar Kano ta dakatar da Mai Unguwar Sabon Gari, Ya’u Muhammad bisa zargin sa da hannu wajen siyar da wata jaririya.
Muhammad Umar, Sakataren Galadiman Kano, Abbas Sunusi ne ya bayyana wannan dakatarwa ranar Talata a Kano, kamar yadda jaridar Intanet, Kano Focus ta rawaito.
Mista Umar ya ce Majalisar Masarautar Kano ta dakatar da Mista Muhammad har zuwa lokacin da Hukumar Hana Fataucin Bil’adama ta Ƙasa, NAPTIP za ta kammala bincike.
NAPTIP tana bincikar Mista Muhammad tare da Kwamandan Hisbah na Fage, Jamilu Yusuf bisa zargin su da siyar da jaririya ga wata ‘yar ƙabilar Ibo a kan kuɗi N20,000
Duka mutanen biyu sun musanta zargin.
Post comments (0)