Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya ce babban burinsa a rayuwa shi ne ya gaji magabatansa kuma yanzu hakan ya tabbata.

Cikin wannan hira ta musamman da ya yi da BBC Hausa, sarkin ya ce baya ga murnar gadar mahaifinsa da yake yi yana kuma murnar zaɓarsa da Allah ya yi domin ɗaura masa nauyin taimaka wa al’ummarsa.

Ya bayyana haka ne yayin da ake shirin bikin ba shi sandar girma, yana mai cewa a halin yanzu murna biyu yake yi.

Kazalika sarkin ya bayyana matakan da ya ɗauka wajen sasantawa da ‘yan uwansa waɗanda suka nemi sarautar tare.

Leave a Comment

%d bloggers like this: