play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Ilimi
  • keyboard_arrow_right Ranar komawa makaranta na wasu jami’ar Bayero

Labarai

Ranar komawa makaranta na wasu jami’ar Bayero

Bello Sani January 6, 2021 12


Background
share close

Wasu jami’o’in gwamnati a Najeriya sun fara shirye-shiryen koma wa makaranta daga ranar 18 ga watan Janairun 2021.

Hakan na zuwa ne bayan janye yajin aikin da aka shafe dogon lokaci ana yi a ƙasar, sakamakon daidatawa tsakanin gwamnatin Najeriya da ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta ASUU a ƙarshen watan Disamban da ya gabata.

Majalisar Sanatocin kowace jami’a ne yake da hurumin sanar da ranar komawa bayan janye yajin aikin, kuma ta kan yi hakan ne bayan gudanar da taro don sanya ranar.

Jami’o’i sun shafe tsawon wata tara a kulle sakamakon yajin aiki da kuma dokar kullen annobar cutar korona da ita ma ta kawo cikas a fannoni da yawa, ciki har da na ilimi.

Yajin aikin ya samo asali ne saboda gaza biya wa ASUU buƙatun da ta nema a wajen gwamnatin tarayya tun a shekarar 2019.

Duk da cewa an janye yajin aikin a ranar 23 ga watan Disamban 2020, to dole sai makarantun sun jira matakan da Kwamitin Shugaban Ƙasa Mai Yaƙi da Cutar Korona zai ɗauka, a yayin da ƙasar ke fama da hauhawar cutar.

Ga dai wasu daga cikin jami’o’in da tuni suka tsayar da ranar komawarsu.

Jami’ar Bayero Ta Kano (BUK)

A wani taro na musamman da Majalisar Sanatocinn Jami’ar ta gudanar ranar Litinin 4 ga watan Janairu, ta amince da kammala shekarar karatu ta 2019/2020 wadda annobar cutar korona ta yi wa tutsu.

Hakan ya biyo bayan wani gagarumin sauyi ne da aka yi wa tsare-tsaren karatun.

Ga dai yadda abubuwan za su kasance:

Masu karatun digiri na farko za su fara ranar Litinin 18 ga Janairun 2021, sai su kammala zangon karatu na farko ranar Litinin 26 ga Afrilun 2021.

Sai kuma su fara zangon karatu na biyu ranar Litinin 3 ga watan Mayun 2021, sai a rufe zangon ranar 16 ga Satumban 2021.

Sannan hukumar jami’ar ta bayar da tabbacin cewa za ta bi dokoki da matakan hana yaɗuwar cutar korona.

Ga masu karatun digiri na biyu da digirin-digirgir kuwa za su fara zangon farko ne ranar 18 ga Janairu sai su gama shi ranar 5 ga twatan Yunin 2021.

Sai kuma su koma zango na biyu ranar 7 ga Yuni a kammala shi ranar 11 ga Satumban 2021.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *