play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Tsaro
  • keyboard_arrow_right OPC, IPOB da Boko Haram duk abu daya ne, babu banbanci, Dambazau

Labarai

OPC, IPOB da Boko Haram duk abu daya ne, babu banbanci, Dambazau

Bello Sani April 10, 2021 10


Background
share close

Abdulrahman Dambazau, tsohon shugaban sojin kasa, ya kamanta kungiyoyin IPOB da OPC da kungiyar Boko Haram.

A cewarsa OPC da IPOB suna yunkurin tayar da tarzomar kabilanci a Najeriya. Ya yi wannan bayanin ne a ranar Juma’a a Abuja, inda Dambazau ya bayyana kamanceceniyarsu da Boko Haram wacce ta fara a 2009.

Ya yi bayani akan yadda suke nuna zakewa da kuma kawo cikas.

“Ba jihohi suke yi wa yaki ba: suna da wata manufar ta daban ta raba kan al’ummar kasar Najeriya. Basu yarda da hadin kai ba kamar yadda Boko Haram take,” a cewar Dambazau.

Kungiyoyin nan biyu suna iyakar kokarinsu wurin tayar da tarzomar kabilanci sakamakon yadda suke kai hare-hare ga ‘yan arewa dake sana’o’insu a kudu don su janyo rabuwar kawuna.

“Hanyarsu daya da Boko Haram, duk masu zakewa ne a wurin amfani da sunan addini don su yi cuta.”

Tsohon ministan cikin gidan ya shawarci ‘yan sanda da su sanya ido kwarai don kwantar da hankula.

“Na yarda da cewa indai aka zage wurin dakatar da ta’addancinsu da rashin tsaro, za a cimma gaci,” a cewarsa.

“Aikin ‘yan sanda ne tabbatar da doka kuma wajibi ne ‘yan sandanmu su motsa akan wannan al’amarin.”

Dama TheCable ta ruwaito yadda IPOB ta jagoranci kashe ‘yan arewa a kudu maso gabas a Najeriya.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *