
Gaba Tsakanin Makota Bello Sani
Ministar Kuɗi ta ƙasa Zainab Shamsuna Ahmed, ta ce za a iya buɗe kan iyakokin ƙasar nan ba da jimawa ba.
Zainab Shamsuna Ahmed ta bayyana hakan ne a lokacin da ta ke zantawa da manema labarai na fadar gwamnatin tarayya a yau Laraba, ta ce kwamitin fadar shugaban ƙasa da aka kafa kan lamarin ya kammala aikinsa kuma ya bayar da shawarar a buɗe.
Ta ƙara da cewa nan ba da ɗaɗewa ba kwamitin zai gabatar da rahotonsa ga shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, daga nan kuma za a gabatar da sanarwa a hukumance kan lamarin.
A cikin watan Agustan shekarar 2019 ne gwamnatin tarayya ta rufe iyakokin ƙasar nan da zummar daƙile yawaitar fasa-kwauri da kuma bunƙasa tattalin arziki.
Matakin rufe iyakokin ya ja hankalin mutane da dama a kasar nan tare da jawo ce-ce-ku-ce, inda wasu ke goyon baya wasu kuma ba sa goyon baya.
A cikin watan Maris din shekarar da mu ke ciki fadar shugaban ƙasa ta ce ‘yan kasar nan sun ga irin amfanin da rufe iyakokin ya yi a fannin tattalin arzikinta.
Malam Garba Shehu, kakakin Shugaba Muhammadu Buhari, wanda shi ne ya bayyana hakan, ya jaddada cewa ba za a bude iyakokin kasar ba sai gwamnati ta samu tabbaci daga wurin makwabtanta cewa ba za a su rika yin abubuwan da suka saba wa doka ba a kan iyakokin.
Copyright Matasa Radio - by Bello Sani
Post comments (0)