play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Kiwon Lafiya
  • keyboard_arrow_right NAFDAC Ta Gano Abinda Ya Janyo Cutar Da Ta Kashe Mutum 4, Ta Kwantar Da 400 a Kano

Labarai

NAFDAC Ta Gano Abinda Ya Janyo Cutar Da Ta Kashe Mutum 4, Ta Kwantar Da 400 a Kano

Bello Sani April 1, 2021 13


Background
share close

Hukumar Kula Da Igancin Magunguna da Abinci, NAFDAC, ta gano abinda yayi sanadin bullar bakuwar cuta a Kano

Makonni biyu bayan bullar wata sabuwar cuta a birnin Kano, Hukumar Kula Da Igancin Magunguna da Abinci, NAFDAC, ta gano abinda ya haifar da cuta a Kano, rahoton The Punch.

A cewar hukumar, wani sinadarin kemikal mai hatsari ne ake siyar da shi da sunan citric acid, wanda ake kira Dan Sanmi, shine ya haifar da cutar wadda ta yi sanadin salwantar rayyuka hudu ya kuma kwantar da mutum fiye da 300 a asbiti.

Shugaban NAFDAC na kasa, Farfesa Mojisola Adeyeye ce ta bada wannan tabbacin a ranar Talata a Kano, jim kadan bayan ta gana da gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje a gidan gwamnati a Kano.

Farfesa Adeyeye, ta yi ikirarin cewa an shigo da sinadarin ne cikin Nigeria ta wani hanya da ba a gano ba aka sayarwa yan kasuwa kan N3000 a maimakon N30,000 wanda shine ainihin farashinsa.

“Kafin yanzu, ana amfani da sinadarin na Dansanmi domin samun dandanon tsami a abubuwan sha, amma a wannan karon guba aka yi amfani da shi a madadin sinadarin da ya yi sanadin rasuwar mutum uku da kuma wasu da suka kwanta jinya.

“Uku cikin abubuwan shan ba su da rajista da NAFDAC, biyu kadai ke da rajista. Abinda ya kamata a siya N30,000 an zo ana sayar da shi N3,000, yayinda wasu na siyar da shi N10,000.”

Adeyeye ta yi alkawarin cewa za a gabatar da sahihin rahoto kan sakamakon gwaje-gwajen da aka yi da zarar an kammala bincike.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *