
Akwai kura bayan NNPC ya ce za a koma saida litar man fetur kan N234 a gidajen mai
Shugaban kamfanin NNPC ya ce dole sai kudin litar mai ya tashi a Najeriya ‘Yan kwadago sun ce ba za su yi na’am da karin farashi a wannan marra ba. […]
Gaba Tsakanin Makota Bello Sani
An kama wata mata yar kasar Kenya mai suna Lucy Njeri an gurfanar da ita a gaban kotu da ke Makadara kan tsohon mijinta wanda a yanzu ta ce auren ya mutu, rahoton Vanguard.
A cewar hujjar da mai karar ta gabatar a kotu, ta yi ikirarin cewa ta dade da cire tsammani kan mijinta domin duk lokacin da ya kusance ta, mazakutarsa na yi mata rauni domin ya yi girma da yawa.
Ta ce daga bisani ta gaji, ta kwashe kayanta ta bar gidasa, ta shaida masa cewa ba za ta dawo ba amma ya cigaba da zuwa gidanta yana domin duba ta duk da barazanar da ta ke masa na cewa ya dena zuwa.
An gano cewa a daren da ta watsa tsohon mijinta, Geoffrey Nyebere, acid, ya tafi gidan misalin karfe 10 na dare a ranar 16 ga watan Janairun 2021 ya fara kwankwasa kofa.
Lucy ta ce tana kan gado tare da saurayinta kuma ta ki bude masa kofa ta umurci ya fice ya bar mata harabar gida amma bai yi hakan ba ya cigaba da kwankwasa kofar, don haka sai ta bude kofa ta watsa masa acid a kirki, ta lalata masa fuska.
Da mutane suka fara taruwa yayin da mutumin ke cikin azaba, matar da saurayinta sun tsere amma an kama su bayan kwana daya.
Shi kuma tsohon mijin an garzaya da shi asibiti don masa magani.
Shugaban kamfanin NNPC ya ce dole sai kudin litar mai ya tashi a Najeriya ‘Yan kwadago sun ce ba za su yi na’am da karin farashi a wannan marra ba. […]
Copyright Matasa Radio - by Bello Sani
Post comments (0)