
Mutanen Arewa fiye da 100 sun tsere daga Imo bayan an hallaka ‘Yanuwansu ‘haka-kurum’
Yan bindiga sun kashe karin mutanen Arewa takwas, yayin da aka ji wa wasu shida rauni a danyen hare-haren da su ka kai a jihar Imo a makon jiya. Jaridar […]
Gaba Tsakanin Makota Bello Sani
An samu fashewar gas a karamar hukumar Amuwo-Odofin na jihar Legas a ranar Talata 12 ga watan Afrilun shekarar 2021, The Punch ta ruwaito.
An gano cewa mutane da dama sun jikkata sakamakon lamarin da ya faru a layin Iyasoko da ke Agboju, Amuwo-Odofin.
An ruwaito cewa lamarin ya faru ne misalin karfe 6.55 na yamma.
Mai magana da yawun hukumar bada agajin gaggawa na Legas, LASEMA, Nosa Okunbor ya tabbatar da fashewar gas din inda ya ce an tura jami’ai masu ceto zuwa wurin misalin karfe 6.50 na yamma.
Ba a tantance adadin mutanen da goborar ta shafa ba a lokacin hada wannan rahoton.
Ya ce, “Eh, da gaske ne. Tawagar jami’an mu suna hanyarsu na zuwa wurin. Cinkoson ababen hawa ne ya sa suka yi jinkiri. Ba zan iya tantance irin barnar da ta faru ba a yanzu.”
Yan bindiga sun kashe karin mutanen Arewa takwas, yayin da aka ji wa wasu shida rauni a danyen hare-haren da su ka kai a jihar Imo a makon jiya. Jaridar […]
Copyright Matasa Radio - by Bello Sani
Post comments (0)