Wata mata mai zama a Kaduna ta bada labarin yadda ta dinga fitar da jini ta baki da hanci bayan an yi mata allurar korona
Wata mazauniya jihar Kaduna mai suna Hannatu Tanko ta bada labarin yadda jini ya dinga fita ta baki da hancinta bayan an yi mata riga-kafin cutar korona.
A wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta, matar wacce ta je neman lafiya a asibitin kwararru na Ashmed dake Kaduna ta bada labarin abinda ta fuskanta.
Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, duk da matar da bakinta tace an yi mata allurar riga-kafin a sakateriyar karamar hukumar Kaduna ta kudu, mutane da yawa sun alakanta hakan da asibitin.
Domin nisanta kansu daga lamarin, shugaban asibitin, Dr Patrick Echobu, yayi jawabi ga manema labarai a ranar Alhamis.
Ya ce matar ta zo asibitin bayan kwanaki shida da aka yi mata riga-kafin a wani wuri na daban.
Shugaban asibitin yace, “A madadin asibitin kwararru na Ashmed, muna nisanta kanmu tare da kushe bidiyon da wata majinyaciya ke yadawa. Ta bayyana kanta a ranar 30 ga watan Maris cewa tana aman jini ta baki da hanci.
“Mun karbeta bayan kwanaki shida da ta yi riga-kafi amma bamu san lokacin da ta fara yi wa jama’a bayani ba har aka dinga yadawa a kafafen sada zumunta.
“Muna so mu sanar da cewa bamu da alaka da abinda ke yaduwa. Ina farin cikin sanar da cewa ma’aikatanmu sun yi riga-kafin.”
Post comments (0)