play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Matasa
  • keyboard_arrow_right Siyasa
  • keyboard_arrow_right Matasa ne ginshiƙin cigaban Najeriya – Atiku Abubakar

Matasa

Matasa ne ginshiƙin cigaban Najeriya – Atiku Abubakar

Bello Sani November 17, 2020 8


Background
share close

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya kuma jigo a ɓangaren adawa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa matasa su ne ƙashin bayan cigaban Najeriya.

Atiku wanda ya yi wa jam’iyyar PDP takarar shugaban ƙasa a zaɓen shekarar 2019, ya ce a kowanne lokaci ina yiwa matasa kallon babban ginshikin ci gaban Najeriya.

Tun da farko Atiku ya bayyana haka ne a yau Litinin cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

“A kowanne lokaci ina yiwa matasa kallon babban ginshikin ci gaban Najeriya, kuma ga dukkan al’ummar da take son ci gaba mai dorewa, ya zama wajibi gareta ta dauki matakan bunkasa rayuwar matasa ta hanyar basu ilimi, ayyukan yi da kare tunaninsu”

“Rashin kyakkyawan tsarin gwamnatoci na inganta rayuwar matasa shi ne ke jefa da yawa daga cikinsu fadawa abubuwan da basu kamata ba”

“Mu duka shaida ne game da abubuwa marasa dadi da suka faru a kasar nan kwanakin baya game da zanga-zangar da ta biyo bayan korafe-korafen Jama’a kan wasu ‘yan sanda dake wuce makadi da rawa yayin gudanar da ayyukan su.”

“Sai gashi ‘yan kwanaki kadan kuma mun sami labarin zargin da ake yiwa wasu ‘yan sanda na Anti-Daba a jihar Kano da kashe wasu matasa biyu ranar asabar.”
“Na karanta labarin a jaridu da dama ranar da abin ya faru, amma abin ya tabbata jiya lahadi bayan da ‘yan sanda suka tabbatar da faruwar al’amarin. ”

“Tabbas wannan al’mari ne mara dadi da takaici. Ina alhinin faruwar wannan al’amari, tare da jajantawa da ta’aziyya ga ‘yan uwa da iyalan wadannan matasa, Allah kuma Ya kare faruwar hakan a nan gaba.”

Hakazalika Atiku Abubakar ya ce ya kamata jami’an tsaro su rungumi tsarin aiki tare da jama’ar gari domin samun nasarar kowar da ayyukan Bata gari.

A ƙarshe ya ce akwai bukatar wayar da kan jami’an game da dabarun aiki ba tare da samun tashin hankali ba.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *