play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Soyayyar Zamani
  • keyboard_arrow_right Matar aure na neman saki saboda mijinta ya kasa yi mata ciki

Labarai

Matar aure na neman saki saboda mijinta ya kasa yi mata ciki

Bello Sani February 23, 2021 3


Background
share close

Wata matar aure, mai suna Marwanatu Muhammad a ranar Litinin ta roki kotun Shari’a da ke zamanta a Rigasa Kaduna, ta raba aurenta da mijinta Iliyasu kan cewa ya gaza yi mata ciki, The Nation ta ruwaito.

A karar da ta shigar, Marwanatu, ta yi ikirarin cewa Iliyasu ya gaza yi mata ciki tunda suka yi aure shekaru 10 da suka shude a 2011.

“Ya taba yin aure a baya amma matarsa ta rabu da shi saboda baya haihuwa. Ina tunanin nawa zai banbanta amma ashe kuskure na yi,
“Lafiya ta kalau ba ni da matsala. Bana ra’ayin cigaba da zaman auren. A shirye na ke in mayar masa kudin sadakinsa, N20,000,” in ji ta.

A bangarensa, Iliyasu ya ce yana bin wacce ta yi karar bashin N17,000 kuma yana son kotu ta taimaka ta karbo masa bashin.

Tunda farko, Alkalin kotun Mallam Salisu Abubakar-Tureta ya umurci ma’auratan biyu su tafi asibiti a musu gwaji domin gano inda matsalar ya ke.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *