
Gaba Tsakanin Makota Bello Sani
Wasu mata guda 30 yan Najeriya da aka shigar dasu kasar Lebanon ta barauniyar hanya sunyi kira ga gwamnatin Najeriya da ta dawo dasu kasarsu ta gado sakamakon matsanancin halin rayuwa da suka tsinci kansu aciki.
Wannan bayanin ya fito daga bakin shugaban gamayyar yan jarida masu kula da sufuri tsakanin kasa da kasa Ajibola Abayomi. Inda yayi kira ga gwamnati wajan gaggauta yin bincike tare da hukunta duk wanda aka samu da laifi.
Shugaban yace an ajiye matan ne su 30 a daki guda mai bandaki mara kyau a garin Dawra dake kasar Lebanon. Daga cikin matan akwai wanda ta fito daga jihar Ondo inda take cewa sun gudo ne daga gidan da suke aiki soboda cin zarafinsu da akeyi ta hanyar yi musu kwacen kayansu, tsefe musu gashi da yi musu aski da reza da kuma hanasu kudinsu na aiki da sukayi.
Tuni hukumomi masu yaki da fataucin bayi na kasashen duniya suka fara bada gudunmawarsu wajan tabbatar da cewa an taimaka wa wadannan mata guda 30 tare da hukunta duk wanda aka samu da laifi.
Copyright Matasa Radio - by Bello Sani
Post comments (0)