
A cikin ƙarshen makon jiya ne wasu masu haƙa su haƙo wani ƙwarangwal mai shekaru 1500 a yankin da ake ci gaba da hakar kabari a tsohon birnin Perre da ke yankin Adıyaman, a kudu maso gabashin ƙasar Turkey.
Birnin Perre na ɗaya daga cikin manyan birane biyar na Masarautar Commagene, wanda ya kasance ƙarƙashin daular Greco-Iranian.
Kamar yadda aka sanar a rubuce aikin tonon da ake yi ne aka gono wani kwarangwal na mutum na miji mai tsawon mita 160.
An sanar da cewa kwarangwal din na lokacin karni na 1500, domin a cikin kabarin anga an sanya abincin matattu a cikin wani kwanon kamar yadda ake yi a wancan al’adar.
Post comments (0)