play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Tsaro
  • keyboard_arrow_right Masu Garkuwa Da Mutane Hanyar Abuja zuwa Kaduna Sun Dawo Aiki

Labarai

Masu Garkuwa Da Mutane Hanyar Abuja zuwa Kaduna Sun Dawo Aiki

Bello Sani July 30, 2020 10


Background
share close

A ranar Alhamis ne masu garkuwa da mutane suka dawo kan babbar hanyar Abduja zuwa Kaduna, inda ake zargin suna ci gaba da garkuwa da matafiya da ba a san yawansu ba.

An samu sauƙin yin garkuwa da matafiya a babbar hanyar tun lokacin da aka hana tafiye-tafiye tsakanin jihohi sakamakon ɓarkewar annobar COVID-19 a ƙasar nan.

Shaidu sun shaida wa Daily Nigerian cewa harin ya afku ne a kusa da ƙauyen Katari da misalin ƙarfe 9:00 na safe.

Mohammed Lawan, wanda ya tsira daga harin, ya faɗa wa Daily Nigerian cewa masu garkuwa da mutanen sun kai wa matafiya masu zuwa Kaduna hari da misalin ƙarfe 8:50 na safe.

“Bai wuce mita 250 kafin mu ƙarasa wajen ba a sai muka tsaya da muka hango su. Na hango Honda CRV 98 Model ƙofofinta a buɗe ba kowa a ciki, alamar da ke nuna cewa sun yi garkuwa da waɗanda suke ciki.

“Daga nan sai muka ji ƙarar bindigu a lokacin da helikwafta ya dira ya mamaye wajen”, in ji Mista Lawan.

Har yanzu ‘yan sanda ba su mayar da martani a kan wannan al’amari ba.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *