
WHO: Zargin alakanta Jemage da corona
Rahoton kwararru a fannin lafiya da suka je binciken silar cutar corona a Wuhan, na cewa akwai yiwuwar Jemage ne ya fara yada cutar ga bil Adama ta hanyar wasu […]
Gaba Tsakanin Makota Bello Sani
Shugaban Hukumar hana Sha da fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA), Brig-Gen. Mohamed Buba Marwa (Mai ritaya) tare da Daraktoci da wasu jami’ai a hedkwatar hukumar ta kasa da ke Abuja a ranar Litinin sun mika kansu ga gwajin shan miyagun kwayoyi.
Mai magana da yawun hukumar, Mista Femi Babafemi, ya ce an yiwa jami’an ba-zata ne lokacin da suka iso wurin aiki, an ba da umarnin rufe kofofin ofishin hedkwatar sannan kuma aka nemi dukkansu su taru a dakin taron hedikwatar.
A cewarsa, a zauren an gayyaci tawagar likitocin da ke karkashin jagorancin Daraktan lafiya na Synapse Services, Dokta Vincent Udenze, wani kwararre a ilimin tabin hankali, da aka riga aka gayyata tare da kayan aikinsu don gwajin ta hanyar daukar samfutrin fitsari.
A wani takaitaccen bayani jim kadan kafin ya fara nasa gwajin, Janar Marwa ya ce gwajin na ba-zata ya zama dole don tabbatar da cewa aikin ya fara daga cikin gida, Daily Trust ta ruwaito.
“Ba za mu iya sanya wasu su yi gwajin shan miyagun kwayoyi ba tare da mika kanmu ga irin hakan ba.
Ya bayyana matakin a matsayin mafari don tabbatar da hukumar ta kubuta daga mambobi masu shan miyagun kwayoyi don tunkarar sauran al’umma.
Marwa ya kara da cewa, “Babban abin da ya sa aka yi gwajin na ba-zata tare da gayyato ma’aikatan lafiya na waje don gudanar da gwajin shi ne kara karfafa ingancin aikin,” in ji shi.
Sakamakon gwajin da tuni likitocin suka fitar ya nuna cewa Janar Marwa tare da Sakataren Hukumar, Barista Shadrack Haruna da sauran Daraktoci a hedkwatar hukumar ta NDLEA duka sun tabbata basa shan kwayoyi.
Rahoton kwararru a fannin lafiya da suka je binciken silar cutar corona a Wuhan, na cewa akwai yiwuwar Jemage ne ya fara yada cutar ga bil Adama ta hanyar wasu […]
Copyright Matasa Radio - by Bello Sani
Post comments (0)