play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Addini
  • keyboard_arrow_right Siyasa
  • keyboard_arrow_right Manyan Arewa su ne matsalar yankin inji Sarkin Musulmi

Addini

Manyan Arewa su ne matsalar yankin inji Sarkin Musulmi

Bello Sani August 26, 2020 8


Background
share close

Mai alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya zargi shugabannin Arewa da cewa ba su da ɗabi’ar gaskiya, iya aiwatar da ayyuka da kuma inganci na ‘gina al’ummar da za ta amfani kowa,’ in ji rahoton jaridar Pivot.

Sarkin Musulmin ya yi wannan magana ne a wurin taron Samar da Tsaro a Arewa da Cibiyar Bincike da Cigaba ta Arewa (ARDP) ta gudanar don ƙaddamar da kwamitin sanya ido kan al’amuran tsaro a yankin arewa, a Kaduna, inda ya ce ba wai Arewa ba ta da hanyoyin warware matsalolin da suke fuskantar yankin ba ne, sai dai rashin ingancin shugabanci ne ya ke daƙlle yankin.

Ya ce shugabannin da su ke cin amanar shugabancin da aka damƙa a hannunsu, za su yi bayani a ranar tashin ƙiyama.

“Muna da tarin takardu da aka tattara a tarukan karawa juna sani aka miƙa wa shugabanni inda aka kai aka jibge su kawai. Muna da maganin matsalolin Arewa.

“Gaskiya ne, ba za a iya magance dukkan matsalolin a lokaci guda ba, don haka, za mu iya aiwatarwa daki-daki. Amma dole in faɗi cewa ba wai mun rasa hanyoyin warware matsaloli ba ne, abin da muka rasa shi ne aiwatarwa da kuma gaskiya. Ba ma gayawa kanmu gaskiya kuma idan har ba mu da gaskiya, za mu cigaba da ɗanɗana ƙuɗarmu.”

Daga nan ya yi kira ga shugabanni, musamman gwamnonin Arewa da cewa su aiwatar da rahotannin taruka da dama aka sha yi don samo mafita ga matsalolin da su ke ƙalubalantar yankin.

Da ya ke tsokaci kan neman kafa rundunar tsaro ta yankin Arewa, ya ce kamata ya yi shugabanni su ja kunnen matasa a maimakon su ƙyale su suna ɗaukar doka a hannunsu.

“Gamayyar Matasan Arewa ta ƙirƙiri rundunar tsaronta da motoci biyu ko uku kawai kuma dattijai suka ƙyale matasan suka cigaba. Shi ya sa na ce masu faɗa aji su ne matsalarmu. Manya su ne matsalarmu.Idan manya ba su yi jagoranci ba, to matasa za su aikata duk abin da suke so kuma suke ganin daidai ne. Ya kamata ku ja kunnen waɗannan matasa ta hanyar ba su kyakkyawan jagoranci,” in ji shi.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *