play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Kiwon Lafiya
  • keyboard_arrow_right Manufofin gwamnatin Buhari sun fi annobar cutar korona Illah

Labarai

Manufofin gwamnatin Buhari sun fi annobar cutar korona Illah

Bello Sani November 17, 2020 9


Background
share close

Ƙungiyar Ma’aikatan Da Ba Na Gwamnati Ba ta Najeriya, FIWON, ta soki Gwamnatin Tarayyar Najeriya bisa yadda ta gaza hana shigo da man fetur zuwa Najeriya, tana mai lura da cewa gwamnatin ba ta cika alƙawarinta na bunƙasa matatun man fetur na cikin gida ba, kamar yadda jaridar Intanet, The News Digest ta rawaito.

Ƙungiyar ta koka bisa tasirin yawan ƙarin farashin man fetur da ake yi wa ‘yan Najeriya, musamman a kan ma’aikatan da ba na gwamnati ba, tana mai lura da cewa manufofin gwamnatin Shugaba Buhari sun wahalar da su fiye da cutar COVID-19.

Da yake jawabi a wani taron manema labarai ranar Juma’a a Abuja, Babban Sakataren FIWON, Gbenga Komolafe, ya ce ma’aikatan da ba na gwamnati ba su amfana da tallafin COVID-19 ba da gwamnati ta raba.

A cewarsa, ma’aikatan ɓangaren noma, samar da abinci da sauransu sun sha wahala matuƙa sakamakon COVID-19, yana mai ƙarawa da cewa da yawansu ba su iya dawowa kasuwancinsu ba bayan an ɗage dokar kullle.

Da yake tsokaci game da ƙarin farashin man fetur na baya bayan nan, Mista Komolafe ya ce: “Abin kunya ne kuma abin kaico a ce Najeriya a matsayinta na ƙasa mai fitar da man fetur za ta riƙa shigo da man fetur, kuma mun yi imanin gwamnatin Buhari ta gaza ta wannan ɓangaren.

“Alƙawarin farfaɗo da tattalin arziƙi da kuma hana shigo da man fetur yana ɗaya daga cikin dalilan da suka sa muka zaɓi wannan gwamnati.

“Ya kamata gwamnati ta zuba jari a matatun man fetur kamar yadda sauran ƙasashen OPEC (Ƙungiyar Ƙasashe Masu Arziƙin Man Fetur) suke yi.

“Hatta Afirka ta Kudu, wadda ba ƙasa ce mai fitar da man fetur ba tana da matatar man fetur. Manufofin gwamnati sun wahalar da ‘yan Najeriya fiye da COVID-19”.

Hassan Hamza

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *