play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Siyasa
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Malaman Islamiyyu a Kano sun sauke Ganduje daga matsayin khadimul Islam

Siyasa

Malaman Islamiyyu a Kano sun sauke Ganduje daga matsayin khadimul Islam

Bello Sani August 26, 2020 10


Background
share close

Tun bayan bullar cutar coronovirus gwamnatin jihar Kano ta dauki matakin garkame makarantun boko da na Allo dama islamiyyu da kuma gidajen kwallon kafa dama gidajen da ake gudanar da bukukuwa da kuma kasuwannin jihar Kano, da nufin kare kai daga cutar ta Coronavirus.

Amma bayan daukar wasu tsawan lokuta a hankali-a hankali za’a iya cewar an bude gurare da yawa amma banda makarantun islamiyyu dana boko.

Haka kuma a baya – bayan nan gwamnati ta bude wasu makarantun bokon da nufin daliban ajin ƙarshe su rubuta jarrabawar WAEC da NECO.

Kusan za’a iya cewa wannan dalili ne ya sa wasu malaman islamiyyu bude makarantun su, amma sai gashi ta gwamnati ta yi umarni da su rufe ko su fuskanci hukunci.

Wasu malaman islamiyyu a yankin karamar hukumar Tarauni a jihar Kano, sun bayyana cewa ya kamata gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya duba wannan al’amari, la’akari da yan da ake masa lakabi da Khadimul Islama ya waiwayi makarantun Islamiyyu domin suna cikin wani hal.

Wani malamin Islamiyya wanda ya bukaci a sakaye sunansa ya ce daga yau sun sauke gwamna Abdullahi Umar Ganduje daga matsayin Khadimul Islama, domin har yanzu ya ki yin wata hobbasa domin bude makarantun Islamiyyu a fadin jihar Kano.

Tuntuni dai gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bayar da umarnin bude gidajen kallon kwallon kafa da gidajen bukukuwa amma kuma har yanzu Islamiyyu sun gagara budewa

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *